MENENE CRYPTOCURRENCY
Kasuwancin cryptocurrency na ci gaba da ha
ɓaka gami da
mamaya tamkar wutar jeji, mutane a sassa daban-daban na
fadin duniya na tururuwar shiga kasuwancin. Adadin masu
amfani da cryptocurrency kullum ƙaruwa ya ke duk da matsin
lamba da
ƙoƙarin yaƙi da shi da Gwamnatocin wasu ƙasashen ke yi. Alherin da ake samu a kasuwancin ya sa al'umma ke tururuwar shiga domin ka da a
yi babu su, wanda suka jima a cikin kasuwancin za ka iya ganin alherin
a bayyane tare da su.