🟣 Pi core team sun sanarda cewa Pioneers sama da miliyan 3.36 sun tsallake KYC
Ayau Pi core team sun sanar da babban ci gaba da aka samu a tsarin KYC, inda ta tabbatar da cewa sama da mutane miliyan 3.36 daga cikin waɗanda suka kasance a “Tentative KYC” sun wuce cikakken KYC bayan sabuwar tsarin bincike da ta ƙaddamar.
Sabon tsarin, wanda yake amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) da manyan bayanai (datasets), yana nazarin bayanan liveness checks da aikace-aikacen KYC domin tabbatar da mutum ɗaya ya mallaki account daya da kuma tabbarda cewa asalin ɗan adam ne, ba na’ura ko fek account ba.
Wannan mataki zezama hanya daga cikin hanyoyin da Pi Core Team zasu ke amfani da shi domin tabbatar da adalci, sahihanci, da tsabtace tsarin KYC cikin sauri.
🟢 🎉🎉🎉🎉
Fiye da mutane miliyan 4.76 da suke a “Tentative KYC” sun samu dama a yanzu ana sake duba KYC dinsu ta wannan sabuwar hanyar.
Daga cikin mutane miliyan 3.36 da suka tsallake akwai kusan miliyan 2.69 anyi musu migration.
Sauran masu “Tentative KYC” kusan miliyan 3 sukuma za su iya samun damar tsallakewa idan suka sake yin liveness check kamar yadda app ɗin ke buƙata.
Pi Core Team ta ƙara da cewa yin Active a cikin app ɗin na iya taimaka wa wasu processes su tafi da sauri, ciki har da KYC da migration.
🟢 Idan KYC ɗinka yana a “Tentative” duk sanda suka bukaci kayi liveness to kayi kokari kayi a lokaci domin hakanne zesa ka tsallake.
#2025goals #migration #pinetwork #passphrase #piappstudio #piiscoming #cryptofuture #pincommunity #pinetworkmedia #pihackathon2025






Charles Egodigwe Egodigwe
Delete Comment
Are you sure that you want to delete this comment ?