Wani yana nan cikin farin ciki a yau saboda ya mallaki wani abu da kai kake ganin ba komai bane a tare dakai daka jima da mallakar sa, ƙila ma baka taɓa tuna ni'ima ce Allah yayi maka ba balle kayi masa godiya akai.
Duk abin da ka rasa a duniya mutuƙar kana tare da Imani tabbas baka yi asara ba. Duk abin da ka samu mutuƙar ya rabaka da Imani tabbas ka yi babbar asara.