Matsalar KYC ɗinka na wucin gadi ko kuma jinkirin samun sakamakon KYC na cikakke da kuma ƙaura zuwa Mainnet na iya zama saboda buƙatar ka kammala wasu ayyuka. Misali, wasu Pioneers suna buƙatar yin karin gwajin tabbatar da rayuwa (liveness checks). Ka tabbatar bidiyon ya kasance a fili tare da kyakkyawan haske. Idan aka nuna maka pop-up don wannan gwajin a cikin manhajar mining, ka yi gwajin ba tare da rufe pop-up ɗin ba.
Ka rattaba hannu kan yarjejeniyar token (token acknowledgment) ko da har yanzu kana jiran sakamakon KYC, saboda yana da muhimmanci ga duk wanda zai yi ƙaura zuwa Mainnet. Wasu kuma dole ne su tabbatar da cewa sun kulle asusun su yadda ake buƙata a cikin Mainnet Checklist.
Ka bincika manhajar KYC ɗinka da kuma Mainnet Checklist ɗinka a yau, sannan ka ɗauki matakin da ake nema domin samun sakamakon KYC naka na ƙarshe da kuma samun damar ƙaurawa cikin gaggawa!
Usman Ismail
Delete Comment
Are you sure that you want to delete this comment ?