Yan Arewa da dama sun fada tarkon zamanin nan — suna yawo da mota, suna sanye da kaya masu tsada, amma cikin zuciyarsu babu makoma, babu aqida, babu aiki na gaskiya da ke gina al’umma.
Matasa da dama sun mayar da kudi tamkar Allah. Duk wanda ke da tsabar kudi — ko ɗan siyasa ne, ko ɗan daba, ko ɗan damfara, ko dan kwaya — shi suke bi, shi suke girmamawa. Sai ka ga matashi mai ƙarfi yana yi wa barawo dariya, yana wa mashayi rawa, yana kiran kansa “hustler” ko “plug.”
Ina Manufarka? Ina Gaskiyar da kake tsaye a kai?
Ko kana rayuwa ne kawai domin daka sha hookah, ka ɗora status, ka wuce?
1. Rayuwar da ba ta da manufa — ba ta da maraba da rayuwar dabba!
2. Kudi ba zai sa ka zama mutum ba — idan babu wani abu da kake karewa, babu wata gaskiya da kake rike da ita!
‘Yan Gaskiya ba su bautar kudi — su na amfani da kudi wajen kare gaskiya!
‘Yan Gaskiya ba su sayar da rayuwarsu ga siyasa ko damfara — sai dai su sadaukar da rayuwarsu domin al’umma!
Sakonmu ga Matasa:
Idan har ka ce kai mutum ne — to girma ba ya fitowa daga yawan kudin da ka tara, sai dai daga irin tafarkin da kake bi, da irin mutanen da kake taya yi wa rayuwa ma’ana!
Ku farka. Ku bijire. Ku tsaya. Ku gina kanku!
Ko kuma ku ci gaba da yawo da kaya masu tsada – a jikinku – alhali a zuciyarku babu komai sai shirme.
✊🏽🔥 Karfin Jama’a - Sabuwar Duniya
#danbello
#yangaskiya
