Saai
Deze post heeft veel feedback van gebruikers gekregen omdat hij eentonig en overdreven repetitief is. DAN BELLO DA ABBA HIKIMA SUN SHIGA KOTU A MADADIN MATASA 231,871 NA N-POWER
A yau, 17 ga Yuli 2025, mun kai gwamnatin Najeriya ƙara a Babbar Kotun Ma’aikata ta Ƙasa dake Abuja saboda kin biyan albashin matasan N-Power da cin zarafinsu da rashin adalci.
Ƙarar me lamba NICN/ABJ/204/20225 na dauke da matasa 231,871 a madadin sauran da suka yi aikin N-Power ba tare da biyansu hakkinsu ba.
ABIN DA MUKA NEMA DAGA KOTU:
1. A biya dukkan alawus da matasa ke bin gwamnati
2. A biya su biliyan ₦5 a matsayin diyyar rauni da aka ji musu sakamakon gaza biyansu
3. A biya miliyan ₦50 kudin dawainiyar shari’a
4. A Ayyana cewa abunda gwamnati ta yi na gaza biyan wadannan matasa bayan su wa n gabatar da ayyukansu, haramun ne, cin zarafi ne kuma ya sabawa dokar kasa da ƙa’idodin aikatau na duniya
Wandanda aka kai ƙara sun haɗa da:
– Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya
– Akanta Janar na Ƙasa
– Attoni Janar na Ƙasa
– Mista Akindele Egbuwalo (Shugaban Shirin N-Power)
Wannan ba wai batun albashi kaɗai bane – wannan magana ce ta mutunci, gaskiya da adalci.
Wanda suka sa hannu:
Barr. Abba Hikima, E. O Ekaun, H.S. Bello Esq, Ridwan Yunusa Esq
(A.A. Hikima & Co., Kano)
Wannan shine mataki na farko.
#npowerlawsuit #yangaskiya #danbelloyace ✊🏽