SUN FARA GIRGIZA!
Rundunar ‘yan sanda ta fitar da sakon gaggawa a ma’aikatar — ta na neman a rufe bakin duk wanda ke magana akan zaluncin fansho.
Bayan shekaru 35 na wahala, mutane suna karɓar Naira miliyan 2. Bayan an ƙwace musu dukiyarsu a cikin tsarin PENCOM — yanzu gwamnati da jagororin ’yan sanda na son su yi shiru?
To ga amsar mu:
✊🏽BA ZAMU YI SHIRU BA.
✊🏽BA ZAMU MU YARDA DA YAUDARA BA.
✊🏽BA ZAMU DAKATA BA.
Rundunar ta yarda da ta yi laifi — ta furta da bakinta cewa akwai matsala, har tana cewa “za a yi bincike.” Binciken me? Me ya fi bayyana fiye da miliyoyin da aka sace wa talakawan jami’ai?
Boring
This post has received widespread feedback from users for being monotonous and overly repetitive.